Yadda Ake Fara Blogging Daga Farko Har Ƙarshe
Blogging yana ba kowa damar yin rubuce-rubuce da wallafa su ta yanar gizo don ilimantarwa, nishaɗi, ko kasuwanci. A yau, blogging ya zama wata hanya mai amfani wajen samun kuɗi, wayar da kai, da kuma ƙirƙirar suna. A wannan rubutu, za mu yi bayani dalla-dalla kan yadda ake fara blogging daga farko har ƙarshe.
Mataki na 1: Zaɓi Wata Ƙwaƙƙwarar (Niche) waton misali topic waton batun da za ka mai da hankali a blog ɗinka. Wannan shi ne mataki na farko kuma mafi mahimmanci. Zaɓi niche ɗin da kake sha’awa ko ka san za ka iya rubutu da yawa a kai.
Misalai: Lafiya, nishaɗi, koyarwa, kasuwanci, labaran yau da kullum, ko fasaha.
Ka tabbatar niche ɗinka yana da masu sha’awa a Najeriya ko duniya baki ɗaya.
Mataki na 2: Zaɓi Dandalin Blogging
Dandalin blogging yana ba ka damar ƙirƙirar blog ɗinka cikin sauƙi. Ga wasu daga cikin dandali mafi sauƙi da inganci:
1. Blogger: Wannan yana da sauƙi ga masu farawa. Ana iya amfani da shi kyauta, kuma yana da haɗin kai da Google AdSense don samun kuɗi.
2. WordPress: Zabi ne mai faɗi wanda yake da ƙarin damar gyara amma yana buƙatar hosting.
A matsayin mai farawa, Blogger na da kyau saboda yana da kyauta kuma ba ya buƙatar hosting.
Mataki na 3: Ƙirƙiri Blog Dinka (A Kan Blogger)
1. Buɗe Asusun Blogger
Je zuwa www.blogger.com.
Yi amfani da asusun Gmail ɗinka don shiga.
Danna "Create Blog" kuma bi matakan da aka nuna.
2. Zaɓi Sunan Blog ɗinka
Zaɓi suna mai ma’ana da sauƙin tunawa wanda ya dace da niche ɗinka. Misali, idan kana rubutu akan girki, za ka iya amfani da sunan “Girman Gidan Girki.”
3. Zaɓi Adireshin URL (Domain Name)
Blogger zai ba ka adireshi kamar example.blogspot.com. Amma idan kana son yin amfani da domain na kanka (example.com.ng), za ka iya siyan shi daga kamfanoni kamar QServers ko DomainKing.
4. Zaɓi Tsari (Theme)
Blogger yana ba ka damar zaɓar ɗayan tsarinsa kyauta. Ka zaɓi wanda ya dace da niche ɗinka kuma mai sauƙin amfani.
5. Yi Gyare-Gyare
Ka daidaita blog ɗinka ta hanyar ƙara “About Us,” “Contact Us,” da kuma “Privacy Policy.” Wannan yana da mahimmanci don samun Google AdSensence.
Mataki na 4: Rubuta Abun Ciki (Content)
1. Zaɓi Taken Rubutunka
Rubuta abubuwan da suka dace da niche ɗinka. Misali, idan kana rubutu kan lafiya, za ka iya rubuta abubuwan kamar "Yadda Ake Maganin Ciwon Kai a Hanya Mai Sauƙi."
2. Rubuta Rubutun Ingantacce
Ka tabbata rubutunka mai kayatarwa ne, cike da bayanai masu amfani, kuma mai sauƙin fahimta.
Ka yi amfani da hotuna da bidiyo don ƙara armashi.
3. Yawaita Wallafa Rubutun
Ka yawaita wallafa sabbin rubuce-rubuce akai-akai don janyo masu karatu da kuma kiyaye su.
Mataki na 5: Inganta Blog ɗinka Don SEO (Search Engine Optimization)
SEO wata dabara ce da ke taimakawa blog ɗinka ya bayyana a kan shafukan bincike kamar Google.
Yi amfani da kalmomi masu mahimmanci (keywords) a cikin rubuce-rubucenka.
Ka yi amfani da meta descriptions da headings (H1, H2, H3).
Ka tabbata blog ɗinka yana da saurin loading kuma ba shi da matsala wajen kallon sa a waya ko kwamfuta.
Mataki na 6: Yadda Ake Samun Kuɗi Daga Blog
Da zarar blog ɗinka ya fara samun masu karatu sosai, zaka iya fara samun kuɗi ta hanyoyi kamar:
1. Google AdSense: Ka nemi shiga shirin talla na Google don samun kuɗi daga tallace-tallace.
2. Affiliate Marketing: Ka tallata kayayyaki ta hanyar amfani da links na kamfanoni.
3. Sponsored Posts: Kamfanoni za su biya ka don wallafa labaransu.
4. Sayar da Kayayyaki: Ka yi amfani da blog ɗinka wajen tallata kayayyaki ko ayyuka.
Mataki na 7: Tallata Blog ɗinka
Don jawo masu karatu zuwa blog ɗinka:
Yi amfani da social media kamar Facebook, Twitter, da Instagram don tallata rubutunka.
Ka shiga cikin forums da groups da suka dace da niche ɗinka.
Yi amfani da hanyoyin backlinks don inganta SEO.
Blogging yana buƙatar lokaci, sadaukarwa, da kuma jajircewa. Amma idan aka bi hanyoyi da tsari kamar yadda aka bayyana a sama, zai iya zama hanya mai ɗorewa don samun kuɗi da kuma yin tasiri. Ka fara yau, ka mai da hankali kan ƙirƙirar abun ciki mai kyau da jawo masu karatu.
Akwai banbanci sakanin blogger da website, dukkansu website ne Amma sunada banbanci Rubutunmu na gaba zamu kawo bambancinsu don a fahimta.
Idan kana da wata tambaya ko kuma kana buƙatar karin bayani, ka sanar da ni. Allah ya taimaka!

Comments
Post a Comment