MAFARKIN YIN KASHI
MAFARKIN YIN KASHI (bahaya)
Asslamu alaikum iyan uwa maza da mata kamar yadda muka saba Gabatarda Karin haske kan mafarkanmu da mukanyi lokuta lokuta, ga wasu kuma sakanyi akai akai, yau ma zanyi bayani kan mafarki da yin kashi wadda mutum zai gani yana stugune kan shadda (toilet) yana kashi kamar a zahiri sai mutum yafarka yaganshi kwance.
Idan aka lura yanayin da mai mafarki yake ciki yanayine na damuwa ko matsasi ko fatara, Samun irin wannan mafarki Ga wadda ke cikin irin waddannan Dana yanayi dana lissafo Abin farin cikine Don mai mafarki zai sami yayewa daga yanayi da ya shiga. Idan talauci yake fama dashi to zai sami sauki ko wadata idan wata damuwane zai fita da ikon Allah.
Mafarki da yin kashi za a fita daga kunci zuwa walwala. Amma idan yakasance mutum yayi mafarki yana kashi kuma yatashi ya taradda kashi a shimfidarsa fa? Amsa wannan baida fassara. Rashin lafiyane sai a nemi magani.
.jpeg)
Comments
Post a Comment