MAfarkin tsallake Rami
Asslamu alaikum iyan uwa maza da mata dafatan kuna cikin halin lafiya ameen.
Yauma ina dauke da muhimmin bayane kan mafarki da tsallake rami da fadawa cikinta, Iyan uwa wasu lokuta mafarkin na sanzawa sakamakon Addu oin mu da mukanyi, ko sadaka Dan shi sadakar yana kawarda fitina da asara da masibu aiwatar da sadaka a yayin mafarki ya nada matukakar faida kwarai da gaske.
musani
Mafarkin da Tsallake rami yana nuni da mai mafarki zai sami nasara kan wani musiba ko matsala ta rayuwa wadda yatunkaroshi.
Idan Dan kasuwa yayi mafarki ya tsallake rami mafarkin na nuni da zai kaucewa asara cikin sana arsa.
Idan Dan makaranta mai rubuta jarrabawa ko gasa ko wani al amari da akeso nasara kansa ya tunkaro shi yayi wannan amafarki zai sami nasara da yardan Allah.
Mafarki da tsallake Rami nasarane da kariya daga sharrin mugunta da gaye.
Idan mutum yaga ya fada rami zai shiga matsaloli na rayuwa,
To amma idan yagani a mafarkinsa yana cikin rami kuma yai nufin fita yanata kokari bai fitaba ya farka,
Wannan yana nunawa za a sha gwagwarmaya kan a fita, amma idan kagani ka fada rami ka fita to yazamto akwai rashi akwai samu Ga Dan kasuwa komai sana a.
Mafarkin Dan kasuwa ya fada rami zai sami faduwa cikin kasuwancin sa ko sana arsa, Allah ne masani.
Mafarki da tsallake rami hawa tudun na sirane kan lamuran rayuwa

Comments
Post a Comment