SIFFOFIN MAFARKAI.
1. Mafarki mai kyau- wannan shine mafarki daga Allah subhanahu wata ala wadda yake bayyana faruwan wani Al amari na mutum ko yake faruwa dashi,
wadda kuma yake siffanta rayuwan mai mafarki wadda zai sameshi nan gaba mai kyau ko mara kyau.
Kuma aduniya ko a lahiransa ,
Mafarki mai kyau daga mahalicci yake wadda yake Zama bushara duniya da lahira.
Ana samun muhimmin mafarki a lukuta muhimmai we adda aka kebesu.
2.mafarki na karya :- wannan shine mafarki daga shedan don shagaltar da ruhin mutum daga tsere wa muhimmin lokaci ko aiki ko sakawa bawa ko kwanto a cikin bacci ya kuma nunama kayan nishadi wadda zai dauke ruhi zuwa kurewan lokaci.
Wannan yanada matukar tsari gamai yin mafarki daya rika kula da lokutan mafarkinsa don kaucewa mafarki wadda bashida makama gareshi da rayuwarsa.
Idan kashagaltu da Munanan ayyuka shedanu zasu samu daman wasa da ruhinka ta yadda zasu rika tsaka maka karya cikin baccinka.
Idan mutum ya nisanshi Allah to shedan ne zai kasance makusanshinsa haka Nan saiya zamto mafarkan na Zama baida makama.
Mafarki baiwa ne kuma haskene dake haskaka maka al amuran rayuwan ka,
Yanada kyau yin addu a idan za a kwanta bacci haka kuma idan akayi mumunan mafarki Nan take ka yi addu a insha ALLAH mafarkin zaiyaye idan na sharrine hakanan idan na alkhairi Ne wadda kake gani Yana nuni alkhairi kana iya neman taimakon ALLAH kan ya tabbatar maka da alkhairin sa sharrin sa ya Kare, haka kuma ana bayar sa sadaka ayayin da akayi mafarki wadda yake taba rai don neman tsari ko tabbatuwan alkhairi.
Sadaka Yana samarwa bawa kariya daga sharri haka Yana toshe hanyar musifu.
.jpeg)
Comments
Post a Comment