Siffan mutanen kirki da ayyukansu.
Siffar mutumin da ya dace mace taso kuma ta kwadaitu da aurensa.
Assalamualaikum iyan uwana maza da mata wannan bayanin zai ilmantar kwarai da gaske wadda ke dauke da sha warwari kan zaman takewa da siffa irin na mutanen kirki wadda yadace ayi mu amala ko soyayya ko zaman takewa na rayuwa, musamman ga mata masu niyyan aure budurwa ko ba zawara.
Kasancewa zamani ko ko ince duniya ko mutane na sanzawa Ako wani Karni ko zamani mutane suna sauya kama hakan yasa don samun abokina kirki cikin mata da maza dole sai anyi taka tsan tsa don gani an samu aboki na gari.
Aboki na gari shine jigon tafiyarka a rayuwa, sa annan musani aboki ko masoyin baya samuwa har sai kaidin ka zamo na gari ba a tambayan halin mutum mu amala da abokan mutum sun ishi Mai lura ya fahimci komai.
Dan haka neke cewa ayi hankali da zamani da aboki a zamani.
siffofin namiji wadda ya dace mace ta mallaka masa zuciya ganin yadda da dama mata wasu kan fada hanun maza bata gari ko gurbatattu masu yin shige cikin riga don su badda sawu daga baya a gane ba mutumin kirki bane cikin wannan rubutun na tabo kadan daga abinnda zaki gane mutum nagari da wadda bana gari ba duk da cewa kowa nada nasa nazari kan hakan. Don haka a karanta a nutse Allah yasa mudace ameen.
Allah madaukaki sarki mai kowa mai duka ya halicci mutane dabamdabam mace dana miji kowa da irin nashi hali, wani halinsa nada kyau wani halinsa bashida kyau sakamakon irin tarbiya daya samu tun yana karami ko sakamakon haduwa da abokai , mutum na zanzawa sakamakon abokai kodai ya zama mai kyau ko mara tarbiya, mutum na iya sanzawa zuwa halin kirki ko halin marakyau sakamakon abokai ko yanayin muhallin dayake zaune. Hakan yasa idan mutum zai yi zama a wuri yakamata ya kulada wadannan abubuwa , na farko muhallin da zai zauna , yadace da rayuwarsa ko addininsa?
Na biyu ya kula da irin mutane dazaiyi mu amala dasu kamar makwabci , aboki
Wannan atakaice.
Idan mutum aka samu ya kula da wannan kaidoji manya sa annan yai kokari cikin addininsa wannan ya dauki hanyar zama mutumin kirki ko mutum na gari,
Wadda ake siffanta mutum da yanayin abokansa, idan kana son ka san halin mutum ka dubi abokansa nan ne zaka samu amsar saninsa nagarine kona banza, bazai yuhu ace mutumin kirki ashe abokansa suna shaye shaye kuma ace shi baya sha ba na biyu,
Saninsa na farko shine duba da siffarsa kamalarsa yanayin suturansa kalamansa harma da annurin fuskarsa da sana arsa.
Wannan shine cikekken gane nauin mutum kuma shine mataki na farko kamun fara tunanin rayuwa mutum Mata kuna son miji nagari, mutum na gari wadda nake nufi shine mai addini ma ana yana kulawa da salloli biyar yana azumi....
Yana da sana a wadda shari a ta amince dashi da abokai nagari , abokai na gari na taka muhimmiyar rawa wajen bada muhimman shawari kan yanayin rayuwa tanan ne aboki ke bada tallafin gani aboki bai fada bakin halin ba.
To me yasaura idan na hango wannan abu ga mutum musamman ya mallaki hankalin kansa yasan yakamata .
Ya kamata ayiruwa da tsaki aga an mallaki wannan mutum a matsayin miji ko abokin hulda.
Idan kika auri mutum irin wadda nai bayaninsa a sama lalle anyi sa an miji.
To idan mace tayi sa an miji meyakamata tayi?
Kodai namiji yai sa a mata to meyakamata yayi?
Dan abinda na fada haka yake ga bangaren mata.
Abinda ya kamata ayi shine kiyaye bacin ran abokin zama da sauke hakkokin abokin zama wadda shari a ya tanadai da kyautata masa Inda hali akara da wadda ma shari a bata ambata ba wadda bai saba kaidai da addiniba , to Amma don sabida rauni na mutane yanzu nauyi da shari a ta ambata ma rabinsa ana kasa aiwatarwa yakamata mukula da hakkokin shari a jan zama da abokin zama miji ko mata.
Sa annan musani Akwai abubuwa dake jawo hankalin abokin zama zuwa gareka na daurashi kan wani hanya mikakkiya daga ciki Akwai shawari maikyau magana Mai dadi,
da yi masa kyauta daga dan wani abu da Allah ya hore maka, hakan na zartar da nauin so da kauna da ba juna shawari wadda suka can canta cikin ilimi da hikima ta yadda rai bazai baciba , da ba juna hakuri ayayinda akaga rai zai baci koya baci.
Hakan yana kara dankon kon kaunar juna da tausayawa a sakani.
Sa annan
Mace yakamata ta zama mai kankan da kai gaban mijinta ,karta zama wadda miji ke zarginta da muggan ayyuka kar ki zama wadda miji kullum yana samun ciwon kai dakei da yin muhawara ko jayayya da shi kullum kan lamari , karki taba yarda da siffar matanda zai wuya rahamar Allah ya samesu wadda suke raba miji da danginsa ta hanyar asirai da daukan sai abinda na zartar shi za ayi idan aka dauki irin wannan to fa ankafurta , ayan Al kurni na cewa
"maza sunada fifiko kan mata"
ma ana maza suna da girma da matsayi kan mata Allah ya ba na miji tunani samada mace komai kankantan namiji Allah ne yaima maza wannan baiwa kuma sune da fada aji kan iyalensu, duk gidan da mace itace keda fada aji to gidan bai dace mutum mai hankali yayi aure gidan ba kuma yanayin gidan zakaga bai burge kowa tarbiya baya isan gidan.
Aurenda mace ke jagoranta baya karko,
Mafi yawan rayuwan aure da gidaje yanzu mata keda fada aji koda bai bayyana a filiba hakan yasa aure baya kargo, ko mace ke jagoranta kasan cewa mata nada dan rauni.
Don haka zan takaita da cewa duk aiki komai kankantarsa wadda zai saka mijinki yaji zai tuna mumunan Abu kanki toki nisanceshi, yin hakan ba Yana nuna kina tsoron sabane a a don tsoron Gamuwa da Allah da kwadayin rahamar Allah.
Don haka nake karawa da,
mutumin kirki namiji ko na kirki kalamansa daban yake,
Suturansa daban yake duk da cewa manzon Allah yayi nuni da Allah baya dubi zuwaga siffarka ko suturarka saidai Yana dubi zuwaga zuciya, dalilin wannan kar ka dauka sai mutum yasaka kaya mai tsada shine mutumin. Kirki a a abin nufi adubi suturarsa shine shiga ta Kamala ta wadda bata siffan tashi mutanen banzaba, Haka kuma Tafiyarsa daban yake ma ana batakama ko nuna girman Kai Allah bayason mutum Mai takalma a bayan kasa,
Sautinsa muryansa daban yake : ba a bukatan mutum Mai magana da akara mara misali,
Ba a samunsa da sonkai,
Baya karya,
Baya kuma yaudara,
Baya ashariya.
Don haka kofofa ka acikin al uma.
Don haka kofofi nada yawa na budi da neman kariya da daukaka a rayuwa, wannan shima daya yake daga wasu kofofin samun haske da daukaka acikin al uma.
Ana samunsu gwargodon iyawa abinda na lissafo idan akai dace aka tarbiyantar da kai aka zama na gari mace kona miji in Allah yaso za a sami abokin zama daza a fahimci juna.
.jpeg)
Comments
Post a Comment