Hanyan samun mijin aure




Asslamu alaikum Iyan uwana mata,

 Aure Nada muhimmancin gaske wadda 
Kusan duk wadda kagani kaso 99.8 daga aurene kuma yanada cikar kamalar mutum da mutunci sa haka yasa mukayi wasu nazari cikin ilimi kan yadda ya a cimma matsayi na aure a rayuwa, wadda rashin aure Yana matukar tayar da hankali musamman wayadda sukeda lafiya kuma suke so suyi riko da sunna na manzon ALLAH sallalahu aihiwasllam.
Kuma a lada na ibada ma aurata sunfi samun kasu na lada Mai yawa.
basaina fada ba musamman Ga wadda yakeda lafiya mace kona miji.

 Duk wata albarka ana samun sa a aure to amma samun Auren ko yin Auren baya samuwa.
Cikin wannan bayani zanyi Akwai mafita don cimma bukatu na aure.

Lalle aure Nada tsada ko kuma ince yayi wuya ko yana wuya ko kuma yai ma wasu matan wu ya ko iyar wuya.  Musani aure batada wuya sai iyadda ka daukeshi. Kuma baida tsada sai yadda aka tsananta, Mata da dama sunaso su sinci Kansu gidan aure, 
Amma abin takaici saidai sugani sunyi aure a mafarki wani abin haushi harda aihuwa Amma a zahiri abin Yaki,

To make haddasa hakan to kubiyoni cikin wannan shafin zan kawo dalili da magani yadda za a magance matsalar.


Kwadayin aure ya faru
 amma hakan yaki faruwa kodai sakamakon wani laluri  ba rashin lafiya da makaman tan haka.  Wasu kuma kama kama lamarin yabi ruwa. Wata kwatakwata bata samun mai mata zancen auren ma kisani lokacinda kikayi I wasa da aure aure saiyayi wasa da kei hummm, 
Wasu kan samu damar aure Amma sai suki ko su Munana lamarin lokacin da taso abin sai kuma yayi wuya.
Aure da taurarin mutum yake tafiya.


--Wata ta rasa aure sabida rashin kyan
Halayyanta (Mugun hali)
--wata kuma ta rasa aure sabida rashin iya kalamanta.
--wata ta rasa aure a dalilin rashin tarbiyar.
--Wata kuma ta rasa aure a dalilin tsabta.
Gasunande da dama wani lokaci mutum na iya gano matsalarsa da kansa.

To tambaya idan na gane matsalana me zai hana nagyara nakuma salami wannan bakin halin har abadan tunda shine silar Koma bayana?

Kamar yadda nace:
 Wata kuma ba kyau ta rasaba duk da cewa mazan zamani da dama daga cikinsu suna son mace maisura mai kyau . amma sai mu duba idan kyau kadai na saka mace ta samu miji da  dama wasu sunyi auren,
Saikaga mace takai mace Amma shuru duk da wani lokaci ana danganta abin da jinnu wasu kuma asirai. to shin aka ne kodai?
Gaskiyadai ba lalle hakanba Koda Yana faruwa Akwai matakai da mutum yakamata ya dauka ma kansa don kubutarda kansa daga tarkon shedan.
Musani
 wani lokaci yin aure bashida tasiri da kenki ko kudinki abinda zai sanya mace tayi saurin samun miji da wuri shixanyi bayaninsu a gaba. Misali idan zamu auna zamunan iyayenmu komin munin mace tana samun aure wadda ma lokacin ba wayewa sosai. 

Amma a hakan ake auransu kuma asamu zaman lafiya kuma miji zaba musu ake kuma su amince bazaka ji wani korafi irin Na yanzuba. Duk da wasu sun fassara hakan a matsayin iyaye na tauyewa iyaiyansu encin zaban abinda suke so wadda daga bayabaya ake fassara mutuwar aure da nauin aurawa mace majin da ba zabintaba. Har ansamu malamai wasu sunaga gara abarsu su fidda wadda sukeso a aura musu. An dauki wannan mataki iyaye naji sunagani Ga wadda ya dace iyarsu ace ta aura wadda yadace da tarbiyar gidan, a yayin haka saita bijiro da wani shirmen mutum wadda ita kanta in ance ta bada labarinsa sai kunya ya kamata amma tanace sai shi. Lamarin a haka aketa tafiya iyan mata suke da ikon iyaye ba iyaye ke da ikon iyaiya ba haka lamarin ke tafiya yanzu, wadda idan aka matsa sai kaga yara Na kokarin lalacewa da shiga duniya. Yana daga dalilin wasu iyaye suna taka tsansan da bacin ran iyaiyansu don gudu karsu shiga wani hali, Amma yanzu da dama iyaiya basa taka tsansa da Bacin ran iyayensu.

 Yanzu wannan tsarin yayi kuwa?

 Zaki aihufa kuma kaima zaka aihufa. To ana cikin haka ambarwa yarinya daman ta kawo wadda take so amma abin ya gagara. Wasu Na cewa matanne sukayi yawa, eih Na yadda mata sunyi yawa amma kisani. Idan kaya tai yawa a kasuwa idan kana so ka daga darajar kayan naka saika ingantashi ka boyeshi cikin Leda tayadda kura bazai lalatashiba, ta hakanne sai kaga ana cewa iyar gidan Malam wane hakika sun sami tarbiya. 
Idan kasin hakafa? To kinga an fara daukan matakin saurin samun mijin aure koba gaskiyaba? Idan ba daidai Na fadaba ko kuma kunada Karin bayani saikuyi comment a can kasa. Idan kika tsarekanki daga mugayen ayyuka kuma kika bi iyaye kika Dage da ibada waton addu a bazaki taba rasa mijin aureba kina cikin gida Allah zai kawo miki mijinki har gida basaima kin sha wahalaba . 


Wasu matan sun dauka shafe shafe ayi haske da saka matsassun kaya don bayyana Suran jiki zai saka ta samu miji a a mace mai wannan tunani aure Na mata wuya, matse jiki da tufafi yana jawo hankalin mazajen banxane gareki. Karkice inbanyi kwalliya Na matse jikiba yaza ayi sugani su yaba inkika dauki wannan salo nafarko zaki haduda wani namiji wadda yasha wankka yabiyoki kizata kin yi sa a kin samu miji a a kanwata kawai yaudaranki zaiyi yaga kin dace da siffar mace dayake nema Dan biyan bukatansa. 
 Da zaki ce masa zamuyi aure zaiyi dariya a ransa Baki sanni bane in yai kokari yace dasauri haka? Kan ki hankare ya gama koda kei Allah ya kiyaye. Don haka kanwata bayan kin kame kanki saiki San wadannan abubuwa guda 

3 zai saka kiyi aure ko ki samu mijin aure da sauri. Nafarko ki iya furta magana mai Dadi da suti madaidaiciya Karki zama kei kullum muryarkine ke sama Dana kowa. Nabiyu ki Iya ladabi ,gaisuwa da yin kara wajen yin magana banda raini. Na uku , karki yarda maza Na wasadake abainan jama a bare a boye, da kame daga zina. Zan fadada bayane kan wadannan abubuwa uku a rubutu Na gaba kucigaba da bibiyana a wannan an shafi. 


 Don haka in Allah yaso ya yarda idan kika dauki wannann mataki daga yau zaki Ga yadda maza zasu taho gareki da aure bada wasaba. Akwai mazajen kirki da suke rokon Allah yabasu mata mai iron wannan suffar kuma zaki samu daga cikinsu wasu Nada dukiya wasu malamai wasu iyan kasuwa da sauransu. Kenan Iran addu ansu Na karbuwa dake zasuyi arangama sai aure. Ko yaya zaki gane namijin dake Neman mata tagari? A rubutu Na gaba zan zano siffarsu.

Comments

Popular posts from this blog

The Rising Shadows: My Prophecies for Blades of the Void

PAWS Token: A Promising Project Launching on TON Blockchain

Dabarun fara Trading coins don kaucewa asara.