Amfanin zogale




Asslamu alaikum iyan uwa maza da mata yau inaso nayi karin Haske da wani Abu daya zama abin afani ga al uma baki daya a duniya ba yanzuba tun daruruwan shekaru da suka cude an san da haka tuni a wannan zamani na yanzu muna kara cigaba da gano muhimman cin abin waton Zogale, A wannan rubutun za a samu ilimi kan amfani da zogale da yadda kwararru ke sarrafa shi daga abinci zuwa magani. Allah ya
Karayi ma zogale albarka ameen. 

Yanzu zamu sunduma cikin bayanin da muhimmancin zogale ga lafiyanmu.

 Dafarko: Zogale wata bishiyace wadda Allah yai masa albarka wadda ake afani da ita don abinci da magani. Zogale kama daga ganye ,itacensa, Hure, iyaiya,man zogale, da sassakensa ko jijiyoyinsa suna taka muhimmiyar amfani ga halittu musaamman mu mutane maza da mata . 

musani ba bakake kadai ke amfani da jogaleba Harda Turawa na sarrafa zogale harcikin wasu magunguna na turawa akwai sinadarin zogale da wasu abubuwan sha wadda ake saidawa akanti ko shago da sauransu. sanin muhimmancinsa da turawa sukayi yasa suke sarrafa zogale wurare dabamdabam, sukan kira zogale da moringa , Akan yi shayin zogale wadda yakeda amfani matuka da tasirin kawarda cutar hawan jini. Yana daga amfanin zogale shine gano wadda sihiri ya sameshi kamar wadda yake fama da cutarda ake zargin sihirine ko maita.



 Ana diban ganyen zogale a murza idan yayi rura a giga ga jikin Mara lafiya idan akwai maita a jikinsa zogalen zaiyi yauki. Haka Allah yayi zogale da abubuwan mamaki da amfani ga al uma , zagole batada hamami ko daci, zogale ana samunta a kasacen duniya da dama, Nigeria nijar, kamaru Ghana, Sudan da wasu kasashen Africa suna shuka zogale. Ana Iya shuka irinsa ko a dasa itacensa zogale yana kamawa matukar wurin nada sanyi.

America na daga cikin kasar da alumar ta ke sarrafa bishiyar zogale da sudi arabiya. Akanyi miya da zogale ko dambu wadda akafi sani da dambun zogale. Har wasu kance dashi macika ko koro. Ana kuma shanya ya bushe ayi miya ko magani da grain zogale. Ga mata masu bukatar ni'ima a jikinsu suna shanyawa a inuwa idan yabushe su daka su hada da Zuma tana sha kan aje shinfida yana saka mace ruwa matuka. 


 Gayen zogale yanada amfani da dama daga ciki ga lafiya yana maganin kan jamau wagon AIDS ta hanyar shanya ganyen a inuwa harsaiya bushe adaka yayi laushi asanya a madara anasha. yana kuma magance cutar typort ta hanyar shan ruwan zogale danye ko tafasacce, haka kuma ana Iya hada ruwan zogale wadda aka tafasa yayi sanyi ba sosaiba asa madara picmilk na ruwa ashanye nan take cikin kofin shayi uku na ruwan zogale amma kar a barruwan ya jima ba a yi amfani dashiba , misali yakai awa daya ba a shaba to wannan ruwan ya baci sai an dafa wani zogalen ayi amfani da ruwan, zogale na warkar da cutar koda. 

Haka kuma yana kashe cutar totonos ayayinda akaji ciwo da karfe amasa ruwan zogale ga ciwon zai warke, basai anyi alluran kashe dafin ba idan anso. Ana magance ciwon ido da zogale ta hanyar diga ruwan zogale a idanda ke ciwo. 

 Cin zogale yana gyara ciki ga wadda cikinsa baida kyau sakamakon basir, haka kuma yana magance wasu kanann shutuka fake jiki , yana kara ma na miji karfi da nishadi a yayin saduwa. Zogale Nada hure shima huran nada amfani haka kuma iyaiyan sa nada amfani wadda da shine ake samun man zogale ana samun manzole a kasuwa .

Comments

Popular posts from this blog

The Rising Shadows: My Prophecies for Blades of the Void

PAWS Token: A Promising Project Launching on TON Blockchain

Dabarun fara Trading coins don kaucewa asara.